Za a farfado da sufurin motocin haya a Abuja

Yayin da babban birnin tarayyar Najeriya Abuja ke ci gaba da bunkasa da mutane, wata matsala da ake fuskanta a birnin ita ce ta sufuri musamman na motocin haya.

Sufuri a birnin dai na da matukar muhimmanci saboda yawan ma’aikatan da ake da su kama daga na gwamnati da ma na kamfanonin masu zaman kansu, wannan ne ya sa sufuri ke da muhimmancin gaske a Abuja.

Bisa la’akari da muhimmancin na sa ne hukumar babban birnin tarayyar, ta karfafa wa kamfaninta na harkokin kasuwanci da masana’antu da sauransu, wato Abuja Investment Company Limited, gwiwa a kan ya farfado da kamfaninsa na motocin sufuri, ta yadda zai rika gudanar da harkokin sufuri a yankin babban birnin tarayyar yadda kamata, kuma da inganci.

Abubakar Maina Sadiq, shi ne babban jami’in kamfanin harkokin kasuwanci da masana’antun na Abuja, ya shaida wa BBC cewa bisa la’akari da muhimmancin sufuri a birnin, ya sa aka fara tunanin farfado da kamfanin sufurin.

Ya ce haka ne ya sa a yanzu suka fara bincike domin gano yawan mutanen da ke birnin da kuma matsalolin da shi kansa sufurin ke fuskanta wajen gudanar da ayyukansa.

Jami’in ya ce za su kuma duba layuka da manyan hanyoyin da ke cikin Abuja, don gano inda jama’a suka fi yawa musamman wadanda ke bukatar motocin sufuri don zirga-zirgarsu ta yau da kullum.

Ya ce yawancin motocin sufurin da ke zirga-zirga a Abuja manya ne, to yawanci rashin hanyoyin da za su rinka bi na da ga cikin abin da ke durkusar da harkar.

Abubakar Maina Sadik ya ce “A yanzu suna nazari a kan yadda za a warewa su kansu motocin hanyoyin da za su rinka bi, da kuma tashoshin da za su rinka tsayawa.”

Jami’in ya ce yawanci talakawa ko kuma wadanda ba su da abin hawa ne suka fi amfani da motocin sufuri, kuma sune suka fi yawa a birnin, shi ya sa ake son farfado da harkar sufurin sosai don taimakawa mutane.

Abubakar Maina Sadik, ya ce idan har ana so a samu nasara wajen farfado da wannan bangare a Abujan, dole sai na samar wa da irin motocin da ke zirga zirga a birnin titunan da za su rinka bi kasancewar su manya ne.

Sannan kuma a janyo masu zuba jari su shiga cikin harkar ta sufuri sai abin ya fi tafiya yadda ake so.

Ya ce, suna kuma duba yiwuwar kawo mtocin sufuri na zamani wanda ba sa amfani su dizel.

Jami’in ya ce tuni shirye-shirye suka yi nisa na fara inganta harkar sufurin a Abuja kuma nan ba da jimawa ba za a fara ganin canji.

Ana hasashen yawancin rabin ma’aikatan da ke birnin tarayyar ba a cikinsa suke zaune ba, su na zama a unguwanni da garuruwan da ke wajen birnin Abuja, har da jihohi makofta saboda tsadar gidan haya.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...