Jami’ar Abuja ta sanar da shirinta na bude cibiyar koyar da harshen Mandarin da kuma al’adun kasar Sin.
Shugabar jami’ar, Farfesa Aisha Maikudi, ce ta bayyana wannan labari yayin tarbar tawagar daliban sashen koyon aikin jarida da sadarwa daga Jami’ar Tsinghua ta China a jiya Juma’a.
Farfesa Aisha ta bayyana cewa jami’ar na da kyakkyawar alaka da kasar Sin saboda dadaddiyar dangantaka tsakanin Najeriya da China, kuma cibiyar za ta fara aiki nan ba da jimawa ba.
Haka zalika, ta kara da cewa wasu daliban jami’ar Abuja sun riga sun fara koyon kwasa-kwasai na harshen Sinanci, wato Mandarin.