Za a fara jigilar alhazan bana ranar Alhamis

Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON ta sanar da cewa ranar Alhamis 9 ga watan Mayu za a fara aikin jigilar alhazai zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.

Shugaban hukumar, Zikrillah Hassan shi ne ya bayyana haka lokacin da yake sanya hannu da kamfanonin jiragen sama da za su dauki alhazan bana ranar Juma’a a Abuja.

Ya bayyana cewa kamfanonin jiragen da za su dauki alhazan sun hada da Azman, Max Air da kuma Flynas na kasar Saudiyya.

More from this stream

Recomended