
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Mohamed Salah ya ci wa Liverpool kwallo a wasan da ta yi nasara da ci 3-1 a kan Manchester City a karawar baya da suka yi cikin watan Nuwamba
An bai wa Manchester City izinin karbar bakuncin wasan Premier League da za ta yi da Liverpool ranar 2 ga watan Yuli a Etihad, maimakon filin da bana kowa ba.
Tun farko an tsara yin wasan a gidan da bana kowa ba don daukar matakan kare lafiya ganin magoya bayan kungiyoyin biyu za su iya taruwa a wajen filin Etihad.
Sai dai kuma kawo yanzu mahukuntan birnin City sun gamsu cewar za a iya buga wasan ba tare da wata matala ba.
Liverpool za ta lashe kofin Premier a karon farko tun bayan shekara 30 idan har City ta kasa doke Chelsea ranar Alhamis a Stamford Bridge.
An hana magoya baya su halarci karawar da ake yi ba ‘yan kallo ko kuma su taro a bayan ginin filin wasan saboda tsoron yada cutar korona.
Ranar 17 ga watan Yuni aka ci gaba da wasannin Premier League, wacce aka dakatar da ita tun cikin watan Maris.