An bayyana cewa za a binne marigayi Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, a Abuja ranar Juma’a mai zuwa, kamar yadda iyalinsa suka sanar.
Wan marigayin, Moshood Lagbaja, ya bayyana hakan ne a garin Osogbo, babban birnin jihar Osun, yayin wata ziyarar ta’aziyya da Ƙungiyar Tsoffin Daliban Makarantar St Charles Grammar School Osogbo (SCOBA) suka kai masa.
Moshood ya bayyana cewa sojoji ba za su iya miƙa gawar Lagbaja ga iyalinsa ba, amma ya tabbatar wa da baƙin cewa za a yi masa jana’iza mai kyau a Abuja ranar Juma’a.
Da yake magana a madadin SCOBA yayin ziyarar ta’aziyyar, shugaban tawagar kuma Mataimakin Shugaban ƙasa na ƙungiyar tsoffin daliban, Injiniya Adesina Salami, ya bayyana marigayi Lagbaja a matsayin mutum na musamman, mai alfahari da makarantar Charlean, kuma shahararren jagoran soja wanda ya yi wa ƙasa hidima da sadaukarwa ba tare da gajiyawa ba.