‘Za a ƙara wa ƴan bautar ƙasa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara musu alawus alawus na wata da zarar ma’aikatan gwamnati suka fara karbar sabon mafi karancin albashin da aka amince da shi.

A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun mukaddashin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na NYSC, Caroline Embu, Birgediya Janar Ahmed ta bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da take jawabi ga matasan a sansanin wayar da kansu na jihar Kebbi da ke Dakingari da kuma na jihar Sokoto da ke Wamakko. 

Ya kuma bukaci ’yan bautar kasar da su kasance masu hakuri da kuma ci gaba da bayar da gudunmawa mai girma ga ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin kasa, yana mai jaddada cewa an yaba da kokarin da suke yi.

D-G ya kuma karfafa musu gwiwa da su yi amfani da mafi kyawun shekarar hidimarsu ta hanyar mai da hankali kan ci gaban kansu da kuma tsara yadda za a samu nasara a nan gaba.

More News

Atiku ya bayar da tallafin miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya bayar da gudunmawar naira miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri babban birnin...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

Mutanen Sokoto na ta murnar kashe ƙasurgumin ɗanbindigar nan Halilu Buzu

Mazauna yankin Sokoto da kewaye na murnar kashe wani kasurgumin shugaban ‘yan bindiga, Kachallah Halilu Buzu, da sojojin Najeriya suka yi a farmakin da...