Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Ghana ya ziyarci Tinubu

Zaɓaɓɓen shugaban kasar, Ghana John Drammani Mahama ya ziyarci shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu a fadar Aso Rock.

Mai taimakawa shugaban kasa Tinubu kan soshiyal midiya, Olusegun Dada shi ne ya bayyana haka a cikin wani sako da ya wallafa a ranar Litinin.

Ziyarar na zuwa ne biyo bayan sakon taya murna da Tinubu ya aikawa Mahama bayan nasarar da ya samu a zaɓen ƙasar da aka gudanar ranar 7 ga watan Disamba.

Mahama wanda ya kasance shugaban kasar, Ghana daga shekarar 2012 ya zuwa 2016 ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da ya tsaya a ƙarƙashin jam’iyarsa ta NDC da kaso 56.55 na kuri’ar da aka kaɗa.

Babban abokin takararsa, Mahamudu Bawamia na jam’iyar NPP wanda shi ne  mataimakin shugaban ƙasar, shi ne ya zo na biyu a zaɓen da kaso 41.6 na kuri’un.

More from this stream

Recomended