Zaɓaɓɓen Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Borno Ya Mutu

Dr Nuhu Clark zaɓaɓɓen dan majalisar dokokin jihar Borno daga karamar hukumar Chibok a zaɓen 2023 ya mutu.

Kamfanin Dilllancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa marigayin ya mutu ne a India inda ya je a duba lafiyar sa.

Babakura Abbajatau, kwamishinan harkokin cikin gida,al’adu da kuma yaɗa labarai na jihar Borno shi ne ya tabbatar da mutuwar a wata tattaunawa da yayi da manema labarai ranar Laraba a Maiduguri.

A yayin da yake jimamin rasuwar mataimakin gwamnan Borno,Umar Kadafur ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga iyalan mamacin, al’ummar kudancin Borno dama jihar baki ɗaya.

Marigayin ya rike muƙamin kwamishinan ma’aikatar rage raɗaɗin talauci kafin ya ajiye ya tsaya takara a zaɓen 2023.

More News

Jihar Neja za ta riƙa biyan  ₦80,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Gwamnan jihar Neja, Umar Bago ya amince a riƙa biyan ₦80,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar. Gwamnan ya amince da fara biyan...

Jam’iyar NNPP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin jihar Kano

Jam'iyar New Nigeria People Party NNPP ta lashe zaɓen  dukkanin kujerun ƙananan hukumomin jihar Kano 44. Farfesa Sani Malumfashi shugaban hukumar zabe mai zaman kanta...

Jam’iyar NNPP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin jihar Kano

Jam'iyar New Nigeria People Party NNPP ta lashe zaɓen  dukkanin kujerun ƙananan hukumomin jihar Kano 44. Farfesa Sani Malumfashi shugaban hukumar zabe mai zaman kanta...

Wani sojan ruwan Najeriya ya hallaka abokin aikinsa a Zamfara

Hedikwatar Tsaron Najeriya ta kama wani sojan ruwa mai suna A. Akila bisa zarginsa da kashe abokin aikinsa.An tura Akila zuwa sansanin Forward Operating...