
Dr Nuhu Clark zaɓaɓɓen dan majalisar dokokin jihar Borno daga karamar hukumar Chibok a zaɓen 2023 ya mutu.
Kamfanin Dilllancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa marigayin ya mutu ne a India inda ya je a duba lafiyar sa.
Babakura Abbajatau, kwamishinan harkokin cikin gida,al’adu da kuma yaɗa labarai na jihar Borno shi ne ya tabbatar da mutuwar a wata tattaunawa da yayi da manema labarai ranar Laraba a Maiduguri.
A yayin da yake jimamin rasuwar mataimakin gwamnan Borno,Umar Kadafur ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga iyalan mamacin, al’ummar kudancin Borno dama jihar baki ɗaya.
Marigayin ya rike muƙamin kwamishinan ma’aikatar rage raɗaɗin talauci kafin ya ajiye ya tsaya takara a zaɓen 2023.