Yan sanda a ƙasar Sweden sun tarwatsa taron masu zanga-zangar bayyana rashin goyon bayansu ga yunƙurin ƙona al Qur’ani mai tsarki.
Hakan dai ya faru ne a birnin Malmo na ƙasar.
Gungun mutane ne suka haɗa gangami a wani dandali inda wani ɗan iraqi ya fito ya ce zai kona littafin mai tsarkin.
Kafofin yada labaran ƙasar sun ce nan take aka far masa da jifa da duwatsu, yayin da kuma wasu masu kallo suka yi ƙoƙarin kutsawa cikin ‘yan sanda da ke ƙoƙarin kare shi, ya zuwa yanzu dai an kama mutum biyu.
An sha ƙone Al Qur’ani musamman a ‘yan watannin nan a ƙasar Sweden, kuma gwamnatin ƙasar ta ce tana nazarin hanyoyin da za ta bi wajen ganin ta haramta hakan.