Young Boys da Manchester United: Ronaldo zai buga wasan ran Talata

Edinson Cavani

Cristiano Ronaldo yana cikin ‘yan wasan Manchester United da za ta kara da Young Boys ranar Talata a Champions League.

United za ta ziyarci Young Boys domin buga wasan farko a cikin rukuni a gasar Champions League ta bana.

Sai dai kungiyar ba za ta je wasan da Edison Cavani, sakamakon jinya da yake yi, wanda bai buga mata wasan Premier League ranar Asabar ba.

Dan kwallon tawagar Uruguay ya ji rauni ne a lokacin atisayen tunkarar karawa da Newcastle United, wanda United ta ci 4-1 a karshen mako.

Sai dai Ole Gunnar Solskjaer ya hada da matashin dan wasa Anthony Elanga cikin ‘yan wasa 22 da zai je Old Boys har da mai tsaron raga Matej Kovar.

Ronaldo, kyaftin din Portugal ya ci kwallo biyu a wasa da Newcastle, wanda zai buga mata Champions League a karon farko tun bayan da ya bar Old Trafford a 2009.

‘Yan wasan Manchester United da ta je Old Boys da su:

De Gea da Heaton da Kovar da Bailly da Dalot da Lindelof da Maguire da Shaw da Varane da Wan-Bissaka da Fernandes da Fred da kuma Lingard.

Sauran sun hada da Mata da Matic da Pogba da Sancho da Van de Beek da Elanga da Greenwood da Martial da kuma Ronaldo.

More News

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...

Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki A Ƙarshen 2024

Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024. Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC...

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta É—aure mutumin sa ya yi sama-da-faÉ—i da kuÉ—in marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...