Yau da rana za a yi jana’izar Sheikh Giro Argungu

A yau Alhamis ne za a yi jana’izar babban malamin addinin Musulunci Sheikh Abubakar Giro Argungu wanda ya rasu a jiya Laraba.

An sanar da cewa jana’izar za ta kasance ƙarfe 2 na rana ne.

Shehin malamin dai ya rasu ne bayan wata ƴar gajeriyar jinya da ya yi fama da ita.

A lokacin da yake raye, yana daga cikin jiga-jigan kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a wa Iqamatis Sunnar (JIBWIS) a Najeriya.

Ya shafe sama da shekara talatin yana wa’azin addinin Muslunci a Najeriya, Nijar, Kamaru, Chadi, Burkina Faso da sauransu.

More News

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da motoci masu amfani da iskar gas ta CNG

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin shugaban kasa na samar da motoci masu amfani da iskar gas ta CNG. Shirin an samar da shi...

NDLEA ta kama wani mai safarar miyagun kwayoyi

Hukumar NDLEA dake yaki da hana sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi ta kama wani ɗan kasuwa, Sherif Egbo mai shekaru 40 a filin...

An kai wa gwamnan Kogi hari

Gwamnatin jihar Kogi ta ce jami’an tsaro sun dakile wani yunkurin kashe gwamnan jihar Yahaya Bello a kan hanyarsa ta zuwa wani aiki daga...

Gwamnatin Najeriya za ta biya alawus ɗin N-Power na wata tara

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na fara biyan bashin watanni tara ga masu cin gajiyar shirin N-Power da ke shirin farawa daga watan Nuwamba....