A yau Alhamis ne za a yi jana’izar babban malamin addinin Musulunci Sheikh Abubakar Giro Argungu wanda ya rasu a jiya Laraba.
An sanar da cewa jana’izar za ta kasance ƙarfe 2 na rana ne.
Shehin malamin dai ya rasu ne bayan wata ƴar gajeriyar jinya da ya yi fama da ita.
A lokacin da yake raye, yana daga cikin jiga-jigan kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a wa Iqamatis Sunnar (JIBWIS) a Najeriya.
Ya shafe sama da shekara talatin yana wa’azin addinin Muslunci a Najeriya, Nijar, Kamaru, Chadi, Burkina Faso da sauransu.