Yar gidan Wamakko ta rasu a wurin haihuwa – AREWA News

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aliyu Magatakardan Wamakko ya yi rashin yarsa, Sadiya Aliyu a ranar Alhamis.

Sadiya Aliyu Magatakarda ta mutu ne tana da shekaru 23 a asibitin koyarwa na jami’ar Usman Danfodiyo dake Sokoto lokacin da tazo haihuwa.

An gudanar da jana’izarta da daren ranar Alhamis a gidan tsohon gwamnan dake kan titin Sahabi Dange a unguwar Gawon Nama dake Sokoto.

Limamin masallacin Juma’a na Sultan Bello, Malami Shehu Akwara shi ne ya jagoranci sallar jana’izar.

More from this stream

Recomended