
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Zindzi Mandela, ƴar Nelson Mandela da Winnie Madikizela-Mandela, wadanda suka sadaukar da rayukansu domin yaƙar tsarin nuna bambancin launin fata ta mutu kamar yadda tashar SABC ta gwamnatin Afirka ta Kudu ta ruwaito.
Ta mutu a birnin Johannesburg ranar Litinin tana da shekara 59.
Wani ɗan uwanta ya tabbatar da mutuwarta, in ji tashar ta SABC.
Ita ce jakadiyar Afirka ta Kudu a Denmark a lokacin da ta mutu, amma ba a bayyana abin da yayi sanadin mutuwarta ba.
Wani rahoto da tashar SABC tayi na cewa, “Ƴar tsohon shugaba Nelson Mandela da tsohuwar mai gwagwarmayar samar da ƴanci Winnie Madikizela-Mandela ta mutu a wani asibitin Johannesburgda sanyin safiyar nan.”
Ita ce ƴar Nelson Mandela ta shida kuma ta biyu da ya samu tare da Winnie Madikizela-Mandela.