‘Yan wasan Real Madrid da za su fafata da Valencia

Real Madrid

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Real Madrid za ta karbi bakuncin Valencia a wasan mako na 23 a gasar cin kofin La Liga da za su fafata a Alfredo Di Stéfano ranar Alhamis.

Tuni kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana ‘yan wasa 23 da za su fuskanci Valencia.

Real Madrid tana da maki 59 a mataki na biyu a teburin shekarar nan, ita kuwa Valencia mai maki 43 tana ta takwas.

Kungiyoyin sun fafata a wasa biyu a kakar bana, inda suka tashi kunnen doki a gasar La Liga ranar 15 ga watan Disambar 2019 a gidan Valencia.

Haka kuma sun yi gumurzu a Spanish Super Cup ranar 8 ga watan Janairu, inda Madrid ta yi nasara da ci 3-1.

Bayan wasan Real Madrid da Valencia idan anjima da akwai karawa tsakanin Deportivo Alaves da Real Sociedad.

Ranar Juma’a za a ci gaba da wasa tsakanin Real Mallorca da Leganes, Granada da Villareal da na Sevilla da Barcelona.

‘Yan wasan Real Madrid da za su fuskanci Valencia:

Masu tsaron raga: Courtois da Areola da kuma Altube.

Masu tsaron baya: Carvajal da Militão da Ramos da Varane da Marcelo da Mendy da kuma Javi Hernández.

Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da James da kuma Isco.

Masu buga gaba: Hazard da Benzema da Bale da Asensio da Brahim da Vinicius Jr. da kuma Rodrygo.

More from this stream

Recomended