
Kungiyar yan uwa musulmi ta Najeriya da aka fi sani da shi’a sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa a rikicin da kungiyar Hamas take da Isra’ila.
Ranar Asabar da safe kungiyar Hamas ta kaddamar da hare-hare kan ƙasar Isra’ila bayan da ta zarge ta da kai hari masallacin ƙudus da kuma kan Falasɗinawa.
Kawo yanzu mutane da dama ne suka rasa rayukansu a dukkanin bangarorin biyu.
Tattaki na yan kungiyar ta shi’a ya fara ne da misalin ƙarfe huɗu na ranar Litinin daga Bantex Plaza inda ya kare zuwa fitilar bayar da hannu dake kan titin Ahmadu Bello.