Mambobin kungiyar yan uwa musulmi da akafi sani da yan shi’a da suka fito daga yankin kudu maso yammacin kasarnan sun yi kira ga mutanen dake yankin da kada su zaɓi shugaban kasa Muhammad Buhari a zaben 2019.
Da sukewa yan jaridu jawabi a bakin kofar shiga fadar shugaban kasa ta Aso Rock dake Abuja a ranar Laraba,Muftau Zakariyya jami’in tsare-tsare na shiyar kudu maso gabas ya ce shugaban kasa Buhari bashi dalilin da zai sa ya cigaba da zama akan mulki bayan shekarar 2019.
Ƙungiyar ta zargi Buhari da yin mulkin kama karya inda ta ce baya mutunta doka da oda.
Ƙungiyar ta gudanar da jerin zanga-zanga na neman a sako jagoransu, Ibrahim Elzakzaky wanda ke tsare a hannu gwamnati tun shekarar 2015.
“Munzo ne yau muyi zanga-zanga neman a sako jihar jagoranmu da kuma mu shawo kan gwamnati da ta bi umarnin kotu,” ya ce.
Kotuna da dama ne suka bayar da belin shugaban kungiyar sai dai kuma kuma gwamnati ta cigaba da tsare shi
.