‘Yan sanda sun kubutar da almajiran da aka sace a Zamfara

Asalin hoton, NPF

Rundunar ‘yan sanda a jihar Zamfara ta ce ta damÆ™a wasu Æ™ananan yara 21 da ta kuÉ“utar, bayan mahaifansu sun tura su zuwa karatun Islamiyya amma ‘yan fashin daji suka tare motarsu cikin dare a Æ™arshen mako.

Ta ce Æ™ananan yaran sun fito ne daga Æ™aramar hukumar Bakura a kan hanyarsu ta zuwa ÆŠan Dume cikin jihar Katsina mai maÆ™wabtaka, kafin sace su a ranar Juma’a.

Alƙaluma sun nuna cewa an sace ɗalibai sama da 1000 a cikin shekarar da ta yi bankwana akasari a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da kuma Neja.

A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar Zamfara SP Muhammad Shehu ya fada wa BBC cewa ranar Juma’a daliban su 19 da mata biyu ” sun kawo daidai dajin Kucheri ne ‘yan bindigar suka yi awon gaba da su.”

Ya kara da cewa wasu mutane ne suka bulguta ma hadakar jami’an tsaron yankin wadda ba ta yi wata-wata ba ta tunkari barayin ta kwato su.

SP Muhammad Shehu ya kuma tabbatar da cewa babu ko da yaro daya daga cikinsu da ya samu rauni ko wata matsala yayin artabun, kuma an kubutar da su duka.

Da BBC ta tambaye shi halin da suke ciki sai ya ce “suna cikin koshin lafiya domin an duba lafiyarsu babu wani wanda ke cikin wani yanayi na rashin lafiya.”

“Mun kira jami’an karamar hukumar mulkin Bakura kuma an hannata musu wadannan yaran don mika su ga iyayensu.” Inji SP Muhammad Shehu.

Sai dai ya yi gargadin cewa al’umma su daina tafiyar dare, kasancewar masu satar sun fi ayyuka a lokacin.

Yan awanni kafin sace daliban ranar Juma’a, maharan sun buda wuta a daidai kauyen na Kucheri, inda suka kashe mace daya suka kuma yi garkuwa da matafiya daga motoci 10.

Wata mata da lamarin ya rutsa da su da harsashi ya raunata wa fuska, ta bayyana wa BBC yadda maharan suka kashe ‘yar uwarta.

“Mun taso daga garin Jibiya da karfe huÉ—u na yamma kuma mun isa Funtua da misalin Æ™arfe bakwai da wani abu. Daga nan mun wuto ‘Yankara zuwa garin Kuceri. Ba mu san da su ba saboda suna cikin duhu ne. Kawai sai muka ji Æ™arar harbi a ko’ina,” in ji ta.

Ta kara da cewa direban motar ya ji ana harbinsu, sai ya juya motar zuwa cikin gona, inda ya koma kan titi, amma sai É“arayin suka bi su suka harbe tayar motar guda ta baya.

“A lokacin ne wani harsashi da suka harbo ya zoje ni ga kunchi kuma ya wuce ya bi ta cikin kujera, inda ya same ta a kanta.”

Ta ce saboda harbin, “gilashin motar ya watse kuma ya shiga cikin ijiyata ya yanke ni.”

Daga nan ne direban motar ya wuce da su zuwa garin Wanzamai.

Matar ta ce bayan sun isa Wanzamai sai direban motar ya bukaci jama’a su ba su agaji, “Daga nan sai aka zo da wata mota kuma aka saka ni da waccan wadda aka harba a kai domin a kai mu asibiti a ‘Yankara”.

Ta kara da cewa, “Lokacin da muka isa ‘Yankara mun É—auka harbin da aka yi mata a bayanta ne, sai da muka kai asibiti ne suka duba kuma suka ce a kanta aka harbe ta.”

Ta bayyana cewa ana cikin kulawa da ita abokiyar tafiyarta ta cika: “Ana min dressing, kai kafin a gama min dressing ma rai ya yi halinsa.”

Matar ta kuma ce ba motar su barayin su ka fara tarewa ba.

“Sun fara tare wata mota kuma suka harbi wani mutum guda a kafa cikin motar, inda shi ma ya juyo kuma ya rinka yi ma direbanmu alama da hannu cewa akwai matsala amma da yake dare ne takwas da rabi shi ya sa bai gani ba.”

Ta bayyana cewa bayan da direban motar da suke ciki ya juya, shi ma ya rika kokarin sanar da wasu direbobin matsalar da ke wurin amma ba su gane ba.

“To sun dai kama wadannan motocin kuma har sun tafi da mutanen da ke cikin motocin. Sun kama kusan mota goma ciki har da tireloli.”

Kauyukan Kucheri da Wanzamai na daga cikin wurare mafiya hadari, inda kusan duka hare-haren baya bayan nan a jihar Zamfara a nan ne suke faruwa.

Kauyukan guda biyu makwabtan juna ne, kuma suna tsakanin garin Tsafe na jihar Zamfara da kuma ‘Yankara a jihar Katsina.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...