
Rundunar yan sandan jihar Ogun ta ce jami’anta sun kama wani mai suna, Babatunde Kolawole mazaunin jihar wanda ake zargi da samun sabuwar gawa ta wani mutum Ado/Odo-Ota a karamar hukumar Ota ta jihar.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Omolola Odutola ita ta bayyana haka a cikin wata sanarwa.
Odutola ta ce jami’an kungiyar tsaro ta Amotekum ne suka fara kama mutumin kafin su mika shi ga hannun yan sanda.
Ta kara da cewa mutumin ya yi ikirarin cewa shi mai maganin gargajiya kuma ya na kokarin ya dawowa da mamacin ransa
Ta cigaba da cewa kawo yanzu an gaza gano inda mutumin ya samo gawar.