
Rundunar yan sandan jihar Gombe ta kwato wasu shanu hudu da ake zargin an sace su ne daga wasu gidajen mazauna a jihar ana gab da bikin Babbar Sallah.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Mahid Mu’azu Abubakar shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
A cewar sanarwar an gano biyu daga cikin shanun ne bayan da aka kai rahoton satar shanu ofishin yan sanda na Gona ranar Talata da misalin karfe 10:30 na dare.
Wani mutum mai suna Mallam Jibrin dake zaune a kauyen Gidim shi ne ya kai rahoton cewa wasu mutane sun shiga gidansa inda suka sace shanu da kudinsu ya kai dubu dari bakwai.
Bayan samun rahoton ne jami’an rundunar suka bazama inda suka gano shanun a wani gida da ba a kammala ba a unguwar Nassarawo, shanu hudu aka gano a gidan da ake zargin na sata ne kuma mutumin ya gane biyu daga ciki nasa ne da aka sace.
Har ila yau an gano wata karamar bindiga kirar gida a gidan ya yi da ake cigaba da bincike domin gano barayin da suka tsere.