‘Yan sanda sun ceto mutum 20 daga hannun ‘yan fashi a Jihar Neja

‘Yan sandan Neja sun ceto mutum 20 da ‘yan bindiaga suka yi garkuwa da su sakamakon samamen da suka kai kan sansanin ‘yan fashin daji a jihar da ke tsakiyar Najeriya.

Kakakin rundunar a Neja, DSP Wasiu A. Abiodun, ya faɗa cikin wata sanarwa ranar Lahadi cewa dakarunsu sun kai samamen ne a yankin Anaba da ke Ƙaramar Hukumar Magama.

Bayan fafatawa gami da harbe-harbe tare da ‘yan bindigar, dakaru sun yi nasarar kashe ‘yan fashin tare da Æ™wato shanun da suka sata.

“Ƙarin dakarun da aka tura ciki har da sojoji da ‘yan banga sun fara fafatawa da ‘yan bindigar a kan hanyar shanu da Ibeto kusan tsawon awa biyu a lokacin da maharan ke Æ™oÆ™arin guduwa,” in ji shi.

Daga cikin makaman da aka ƙwace daga hannunsu sun haɗa da bindigar AK-47 ɗaya da ƙunshin harsasai 30 da wayar salula bakwai da babur ɗaya, a cewar DSP Abiodun.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...