’Yan Sanda Sun Ceto Jariri Da Aka Binne a Raye a Jihar Kebbi

Rundunar ’yan sandan jihar Kebbi ta bayyana cewa ta gano jariri da aka binne da ransa a garin Kamba, karamar hukumar Dandi ta jihar.

Mai magana da yawun rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ya ce wani manomi mai suna Alhaji Kabiru Muhammad ne ya gano wurin da aka dan yayyafa kasa kamar sabuwar kabari a gonarsa.

“Ya yi ihu, tare da taimakon mazauna yankin aka tono jaririn, inda aka same shi da ransa. An garzaya da shi asibitin Kamba, inda likitoci suka tabbatar da lafiyarsa bayan samun kulawa,” in ji sanarwar.

Bayan bincike, ’yan sanda sun cafke wata mata mai shekara 20 mai suna Maryam Atiku, wadda ake zargi da yunkurin kashe jaririnta ta hanyar binne ta da ranta a dajin Malam Yaro, ranar 25 ga Yuni, 2025. Rahotanni sun ce Maryam ta daure wuyan jaririn da zani, ta toshe bakinsa, sannan ta binne shi a rami mara zurfi.

Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Bello Sani, ya bayyana wannan aiki a matsayin “na rashin imani kuma abin kiyayya,” inda ya jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci cin zarafin yara ko tashin hankali da ya shafi jinsi ba.

Ya yi kira ga iyaye, masu kula da yara da shugabannin al’umma da su kare rayuwar yara ba tare da bari talauci ko wani matsin lamba ya haddasa musu cutarwa ba. Haka kuma ya yaba da matakin matar gwamnan jihar, Hajiya Zainab Nasir Idris, na tallafawa jaririn, tare da jinjinawa Alhaji Kabiru Muhammad bisa jajircewarsa wajen ceton rayuwar jaririn.

Sanarwar ta kara da cewa, “Za a gurfanar da wacce ake zargi a gaban kotu domin fuskantar shari’a da nufin zama izina ga wasu.”

More from this stream

Recomended