‘Yan sanda a Najeriya sun cafke matashin mawaki, Tekno, mai shekara 26, saboda yin rawa da wasu mata “kusan tsirara” a cikin wata babbar mota a birnin Legas.
Motar dai na da gilashi mai haske a bayanta abin da ya bai wa mutane damar ganin masu yin rawar a lokacin da na’urar bayar da hannu ta tsayar da su.
‘Yan sanda sun tabbatar da kame fitaccen mawakin, wanda cikakken sunansa shi ne Augustine Kelechi, ranar Talata saboda “yawo da mata kusan tsirara” a yankin Lekki na birnin.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Legas ya ce an kuma kama wasu mata biyu.
Mawakin, wanda ya fito a kundin wakar da mawakiyar Amurka Beyonce ta fitar a kwanan nan, ya jefa mutane da dama cikin dimuwa bayan da ya shiga cikin wani abu da ya yi kama da tallan gidan rawa na tabara – wanda a kan yi tsirara.
Matafiya akan titi sun yi mamakin ganinsa yana tikar rawa a motar wacce ana iya ganin abin da ke faruw a cikinta.
An kuma ganshi yana lika wa matan kudi a wani bidiyo da aka wallafa a intanet.
Mazauna birnin sun nuna fushinsu a shafin Twitter, sannan hukumar kula da tallace-tallace ta dakatar da kamfanin da ya shirya “tallan”.
Tekno ya nemi afuwa kan abin da ya yi, sai dai ya musanta cewa tallan gidan rawa ne.
Ya ce “Muna daukar bidiyo ne na wata waka, sai muka fuskanci karancin motocin da za mu dauki mutane zuwa wurin da za mu je.”
‘Yan sanda sun ce “irin wannan aiki na tabara a bainar jama’a” ya sabawa doka, inda mai magana da yawunsu ya ce za a gurfanar da wadanda aka kama a gaban kotu.