
Rundunar yan sandan jihar Kebbi ta kama wani mutum mai suna Saidu Sani wanda aka fi sani da Dankahuwa kan laifin yiwa wata yarinya fyade mai suna Amina Isiya a karamar hukumar Aliero ta jihar.
A cewar yan sandan wani danuwan yarinyar ne mai suna Yushau Adamu ya kai rahoton faruwar lamarin wurin yan sanda.
Wanda ake zargi ya hilaci ƙaramar yarinyar zuwa ɗakinsa inda ya yi lalata da ita.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar a cikin sanarwar da ya fitar ya ce wanda ake zargi bayan ya aikata fyade ya yi barazanar kashe yarinyar idan ta fadawa wani abun da ya faru.
Ya kara da cewa tuni aka shirya gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.