‘Yan Sanda A Jihar Kano Sun Kwace Tabar Wiwi Ta Fiye Da Naira Milyan Shida

‘Yan Sanda A Jihar Kano, Sun yi Nasarar Kwatar Tabar Wiwi Wacce Kudinta Ya kai Naira Milyan Shida Da Naira Dubu Dari Shida Da Goma Sha Biyar (6,615,000).

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Bakin SP Magaji Musa Majia, Ya ce Sun Sami Bayanen Sirri Ne Kan Inda Aka Boye Tabar A Unguwar Tudun Wazirci Da Badawa Duk A Cikin Birnin Kano. Kuma Cikin Ikon Allah Da Suka Tsananta Bincike Sai Suka yi Nasarar Samun Kayan Laifin, Amma Ba su Samu Mai Kayan ba.

Sai Dai Yace Yanzu Haka Suna Kan Bincike, Inda Kuma Za su Mika Tabar Zuwa Kotu Domin Neman Izinin Kotu Ta Halarta musu Domin Kone ta.

More News

Gwamnan Kebbi ya raba motocin alfarma ga sarakunan jihar

Gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris ya miƙa kyautar mota ƙirar Toyota Land Cruiser ga sarakuna huɗu na  jihar masu daraja ta ɗaya. An miƙa muƙullan...

Kotu ta bayar da belin tsohon gwamnan Taraba Darius Ishaku kan naira miliyan 150

Babbar kotun tarayya dake zamanta a Maitama a Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku kan kuÉ—i naira miliyan 150. A...

Ƴan sanda sun kama mutane 4 da suka sace kayan tallafin ambaliyar ruwa a jihar Borno

Rundunar Æ´an sandan jihar Borno ta ce ta kama mutane huÉ—u da aka samu da sace kayayyakin tallafi da aka bawa mutanen da ambaliyar...

TIRƘASHI: NDLEA ta yi babban kamu a Kaduna

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar Kaduna, ta ce jami’anta sun kama wasu haramtattun abubuwa da suka kai...