Daga Sabiu Abdullahi
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Gombe ta kama wasu matasa guda biyar bisa zargin hannunsu a kisan wani mutum bayan wata gardama a taron biki da aka yi a kauyen Jauro Ali.
Wadanda ake zargin su ne Jauro Babawuro (17), Yayaji Bello (16), Baffaji Adamu (16), Babangida Dotti (18), da Yaya Bapati (17). An kama su ne bayan mahaifin mamacin, Dotti Manu, daga kauyen Wuro Wandara ya kai rahoto.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda, Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Disamba, 2024, misalin karfe goma na dare.
A cewarsa, gardamar da ta taso tsakanin wadanda ake zargin da mamacin yayin taron bikin ta rikide zuwa tashin hankali, inda matasan suka lakada wa mamacin duka da sanda.
A halin yanzu dai ƴansanda na ci gaba da bincike ken lamarin.