Yan sanda a Calabar sun gano gawarwakin daliban Jami’ar ABU biyu da suka nutse a hatsarin jirgin ruwa

Kwanaki biyu bayan jirgin ruwan dake dauke da daliban koyon aikin likita 14 ya kife a wani ruwa dake Calabar kuma aka ceto 11 daga ciki a yanzu an gano gawarwakin mutane uku daga ciki wadanda a baya aka neme su aka rasa.

Masu iyo daga yankin tare da taimakon yan sandan ruwa su ne suka samu nasarar gano gawarwakin mutanen.

Mutane yankin sun cigaba da neman gawarwakin daliban a baki dayan yinin ranar Lahadi lokacin da suke tsammanin gawarwakin za su yo sama bayan shafe awanni 24 daga lokaci da kuma wurin da suka nutse har ya zuwa ranar Litinin.

A cikin gawarwaki uku da aka gano ranar Litinin akwai MustaphaAminu Tukur da Kabiru Hamza dalibai a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.

Da yake wa manema labarai jawabi a wurin shakatawa na Marina Resort dake Calabar, kwamishinan yan sandan jihar, Gyogon Augustine Grimah ya bayyana cewa ” Da aka hango gawarwakin yan sandan mu na ruwa sun isa wurin tare taimakon mutanen yankin da suka iya ruwa an ciro gawarwakin.”

Tuni gwamnan jihar Cross River ya bayar da umarnin rufe wurin shakatawar har sai an gudanar da bincike.

More from this stream

Recomended