
John Bonzena shugaban majalisar dokokin jihar Taraba ya sauya sheka daga jam’iyar PDP ya zuwa APC.
Sauya shekar ta gudana ne a ranar Litinin gabanin shirin sauya shekar da gwamnan jihar, Agbu Kefas ke yi na komawa jam’iyar ta APC.
Suma sauran masu rike da mukamai a majalisar dukkansu sun bi sawun shugaban majalisar wajen komawa jam’iyar ta APC daga PDP.
Wani fefan bidiyo da ya karade kafafen soshiyal midiya ya nuna yadda yan majalisar ke sauya hularsu ya zuwa hula mai dauke da alamar tafiyar siyasar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Bidiyon ya kuma nuna yan majalisar dauke da tsintsiya dake zama alamar jam’iyar APC.

