Yan fashin daji sun yi garkuwa da wasu iyalai su 7 tare da jikkata ƴan sanda 2 a Abuja

Yan sanda biyu sun samu raunin harbin bindiga a yayin da aka yi garkuwa da wasu iyalai su 7 dai-dai lokacin da yan fashin daji ke cigaba da zafafa kai farmaki a karamar hukumar Bwari dake birnin tarayya Abuja.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa wani mutum mai matsakaicin shekaru da ake kira Alhaji wanda ya yi wa ƴan sandan jagora a ƙoƙarin daƙile yin garkuwa da iyalan ya mutu sakamakon harbin bindiga.

A cewar jaridar a ƴan kwanakin nan yan fashin daji na yawan kai farmaki kauyukan dake karkashin karamar hukumar Bwari inda suke sace mutane tare da kashe wasu.

Wani mazaunin Bwari mai suna Isiah Samuel ya fadawa wakilin jaridar cewa lamarin ya faru da tsakar daren ranar Laraba lokacin yan fashin dajin suka farma unguwar Zuma 1 dake mazabar tsakiyar Bwari.

More from this stream

Recomended