Yan Daba Sun Tarwatsa Masu Zaɓe A Kano

Mintoci kadan bayan da aka fara kada kuri’a akwati mai lamba 030 dake mazabar Kwaciri karamar hukumar Fagge a jihar Kano sai gungun yan daba dauke da makamai suka tarwatsa masu kada kuri’a.

An ga mutane maza da mata suna gudun ceton rai tare da tserewa daga duwatsun da bata garin suke jifa musu.

Amma kuma jami’an tsaro sun yi gaggawar kai ɗaukin gaggawa inda suka fatattaki ɓatagarin tare bada kariya ga jami’an zaɓen kuma komai ya cigaba da gudana dai-dai.

Yaune hukumar zabe ta ware domin gudanar da zaɓukan cike gurbi a wuraren da ba a karasa ba.

More from this stream

Recomended