Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon dan majalissar dokokin jihar Ogun

Yan bindiga sun yi garkuwa da Maruf Musa tsohon mamba a majalisar dokokin jihar Ogun.

Musa wanda ya wakilci mazabar Ogun Waterside daga shekarar 2007 zuwa 2011 a majalisar jihar an yi garkuwa da shi ne a ranar Talata da daddare a Ibiade dake karamar hukumar Ogun Waterside.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi harbi domin tarwatsa mutane kafin suyi awon gaba da dan majalissar lokacin da ake yin Sallah a wani masallaci dake farfajiyar gidansa.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Babaseyi Boluwatife ya tabbatarwa da jaridar The Cable faruwar lamarin.

Boluwatife ya ce tuni aka baza jami’an tsaro domin kubutar da shi.

Ya shawarci al’umma da su kwantar da hankalinsu kana su jira karin bayanai daga hukumomin tsaro.

More from this stream

Recomended