Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 70

Yan bindiga sun harbe mutane hudu tare da yin garkuwa da wasu 70 a wasu kauyuka dake karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto a tsakanin ranar Lahadi zuwa Litinin.

Wata majiya dake yankin ta fadawa jaridar Daily Trust cewa mutane hudun da aka kashe manoma ne da aka kashe a gonakinsu.

Wani tsohon shugaban karamar hukumar, Idris Danchadi ya bayyana cewa yan bindigar sun kuma sace manoma 70.

Ya ce mutane 19 aka sace daga kauyen Tsamaye sai kauyukan Mazau da Marina inda aka sace 11 a kowanne.

Ya kara da cewa yara 7 yayan wani da ake kira Alhaji Malam aka sace daga kauyen Katume 8 kuma daga kauyen Garki da Yar’adua.

Danchadi ya kara da cewa mutane 15 aka sace daga kauyen unguwar Lalle 7 kuma daga Dangawo.

More from this stream

Recomended