
Yan bindiga da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasar da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna sun kara sako mutanen 7 daga cikin mutanen da su kai garkuwa da su.
Mutanen da aka sako sun haɗa da wata mata da mijinta da kuma ƴaƴan su huɗu sai kuma wata dattijuwa mai shekaru 60.
Sunayen mutanen da aka sako sun haɗa da Abubakar Idris Garba da matarsa Maryam Abubakar Bobbo da kuma babban dansu Ibrahim Abubakar Garba mai shekaru 10.
Sauran sun hada da Fatima Abubakar Garba, Imran Abubakar da kuma ƙaramar cikin su Zainab Abubakar Garba.
Har ila yau yan bindigar sun sako Hajiya A’isha Hassan mai shekaru wacce aka sako saboda rashin lafiya da take fama da ita.