Wasu yan bindiga da aka bada rahoton sun yi shigar mata sun kai hari karamar hukumar Maru inda suka sace mutane da ba a san dadinsu ba.
A cewar mazauna yankin yan bindigar sun kai farmaki ne da wajen karfe 7 na dare akan babura inda suka fara harbi kafin su yi awon gaba da mutane ciki har da mata da yara.
Kauyen da aka kai harin na da tazarar kilomita 30 daga karamar hukumar Bungudu inda yan bindiga suka sace mutane 7 a ranar Lahadi ciki har ɗan sarki.
“Ƴan ta’addar sun farma garin babu jimawa da idar da sallar Magriba inda suka fara harbin kan me uwa da wabi. Mutane sun fara gudun tsira inda yan bindigar suka bi su cikin gidajensu i suka yi awon gaba da yawa daga cikinsu.” a cewar wata majiya dake garin.
Majiyar ta kara da cewa duk da cewa ba a san yawan mutanen da suka tafi da su ba yan bindigar sun tafi da akalla mutane 50.