
Yan bindiga sun yi garkuwa da, Matthew Abo Kwamishinan Yada Labarai, Al’adu da Yawon Bude Ido na jihar Benue.
An yi garkuwa da Abo a gidansa dake garinsu na Zaki-Biam a karamar hukumar Ukum ta jihar ranar Lahadi da daddare.
Kwamishinan ya karbi rantsuwar kama aiki ne a matsayin mamba a majalisar zartarwar jihar a ranar 29 ga watan Agusta.
Ya fito ne daga karamar hukumar Ukum da tayi kaurin suna wajen tashin hankali.
Shedun gani da ido sun ce wasu yan bindiga ne akan babura suka sace kwamishinan daga gidansa dake Zaki-Biam kauyen da yayi fice kan kasuwan doya mafi girma a Najeriya.