Yan bindiga sun sace kwamishina a jihar Nassarawa

0

Wasu yan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun sace Mallam Yakubu Lawal Kwamishinan Yada Labarai Al’adu da Yawon Bude Ido na jihar Nasarawa.

Rahotanni sun nuna cewa an sace Lawan ne daga gidansa dake Nasarawa Eggon ranar Litinin da daddare bayan musayar wuta da yan bindigar.

Wani dan uwan kwamishinan da ya nemi a saka ya sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce yan bindigar da suka sace kwamishinan sun zo ne dauke da manyan bindigogi.

Kawo yanzu dai rundunar yan sandan jihar Nasarawa ba ta fitar da wata sanarwa ba kan faruwar lamarin.