Yan bindiga sun sace ɗaliban firamare 6 a jihar Nasarawa

0

Yan bindiga sun sace yara 6 a firamaren LEA dake Alwaza a ƙaramar hukumar Doma ta jihar Nasarawa.

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigar sun sace yaran ne da misalin ƙarfe 07:00 na safe.

Rahman Nansel kakakin rundunar yan sandan jihar Nasarawa shi ne ya tabbatar wa da jaridar The Cable faruwar lamarin.

Nansel ya kara da cewa tuni aka bincike tare kokarin ceto yaran.

Jihar Nasarawa dai na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya dake fama da matsalolin tsaro.