
Yan bindiga sun kona ofishin yan sanda na Affor Atta dake karamar hukumar Njaba ta jihar Imo.
Harin na ranar Talata na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan harin da aka kai kan ayarin motocin tsohon gwamnan jihar Ikedi Ohakim inda aka kashe mutane 4.
A lokacin maharan sunyi amfani da bama-bamai inda suka jefa su ofishin yan sandan sai dai sun yi rashin nasara babu kowa a ciki.
Harin ya jefa zullumi da fargaba ga mutanen yankin inda suka ki barin gidajen su a baki dayan ranar.