’Yan Bindiga Sun Kona Mutane Hudu Da Ransu A Zamfara Bisa Zargin Kin Biyan Haraji

Akalla mutane hudu sun rasa rayukansu a daren ranar Alhamis bayan ’yan bindiga sun kai hari kauyen Gwargwaba da ke gundumar Nahuce a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.

Rahotanni sun nuna cewa ’yan bindigar, wadanda aka ce suna dauke da manyan makamai, sun mamaye kauyen da misalin karfe 6:00 na yamma tare da banka wa gidaje da dama wuta. Mutanen da suka mutu an ce wutar ta kama su ne a cikin gidajensu.

Baya ga haka, maharan sun lalata kayan abinci tare da kashewa da kuma kona dabbobin mutanen kauyen.

Wani masani kan sha’anin tsaro, Bakatsine, ya bayyana a wani sakon da ya wallafa a shafin X cewa harin ya biyo bayan kin amincewar mutanen kauyen na biyan harajin da ’yan bindigar suka kakaba musu.

A cewarsa, kin biyan harajin ne ya fusata ’yan bindigar, lamarin da ya haifar da wannan mummunan daukar fansa.

More from this stream

Recomended