Yan bindiga sun kona gidaje 21 a wani ƙauye dake Kaduna

Wasu yan bindiga a ranar Litinin sun kai farmaki kauyen Kikuba dake Gundumar Chawai a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna inda suka cinnawa gidaje 21 wuta dake yankin.

Yan bindigar sun isa Yankin suna harbin kan me uwa da wabi da misalin karfe 06:30 na yammacin ranar Litinin a cewar hakimin yankin Yahaya Muhammad.

Jaridar ta gano cewa kauyen na da makotaka da jihar Plateau.

Hakimin na Chawai wanda ya kasance a garin Kaduna domin ganawa da kwamishinan ƴansandan jihar shine ya bayyana wa jaridar Daily Trust abin da ya faru a wata tattaunawa.

Ya ce yan bindigar sun kuma kai farmaki kauyen unguwar Rimi inda suka kashe wasu samari uku a ranar da suka kai hari kauyen Kikuba.

“Sun kai farmaki Kikuba da misalin karfe 06:00 na yamma ranar Litinin a garin dake iyakar Kaduna da Plateau. Kauyen na karkashin Gundumar Chawai akalla gidaje 21 aka kone ya yin da mutum guda ya rasa ransa a harin.

More from this stream

Recomended