Yan bindiga sun kashe yan sanda uku a Rivers

0

Akalla yan sanda uku ne suka rasa ransu a wani hari da wasu yan bindiga suka kai musu a jihar Rivers.

Lamarin ya faru ne ranar Alhamis da daddare a Rumuokoro dake karamar hukumar Obior-Akpor dake jihar.

An ce maharan sun sace shugaban wani kamfanin man fetur da iskar gas bayan sun kashe yan sandan da suke bashi kariya.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko ta ce kawo yanzu suna bincike akan lamarin.