Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sanda A Zamfara

Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai a hanyar Gusau zuwa Sokoto a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara sun kashe ‘yan sanda hudu.

A cewar wani dan unguwar mai suna Haruna Musa, ‘yan bindigar sun yi wa jami’an ‘yan sandan kwantan bauna ne a kan hanya a ranar Litinin din da ta gabata.

Musa ya ce ‘yan bindigar sun bude wuta kan jami’an ‘yan sandan da ke wani shingen da suka kafa a wani wuri da ke kusa da garin Bungudu, inda suka kashe hudu daga cikinsu.

More from this stream

Recomended