
Yan bindiga sun kashe wani mutum mai suna, Rabilu Tukur dake kauyen Dan Ali karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina a ranar Lahadi.
Jaridar Daily Trust ta gano cewa an kashe marigayin ne da misalin karfe 1 na rana.
Wani mazaunin Dan Ali da ya nemi a boye sunansa ya fadawa wakilin jaridar Daily Trust cewa marigayin wanda ma’aikacin karamar hukumar Danmusa ne na dawowa ne bayan ya sauke wani mutum a kauyen Tashar Biri.
“Yana amfani da babur dinsa wajen yin acaba inda ya kai fasinja kauyen Tashar Biri yana kan hanyarsa ta dawowa ne lokacin da maharan suka biyo shi suka farmasa da adda a kusa da kauyen Dan Ali da tsakar rana,” ya ce.
Ya kara da cewa yan bindigar sun bi sahun wasu da suka yi kaura ya zuwa kauyen na Dan Ali inda suka kwace musu dabbobi da dama.