Yan bindiga sun kashe wani lauya a Zamfara

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kashe, Ahmad Kwatarkwashi wani jami’in Kungiyar Lauyoyin Najeriya ta NBA a gidansa dake karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Junaidu Abubakar shugaban kungiyar ta NBA shiyar Gusau ya ce yan bindigar sun kai wa marigayin farmaki ne cikin dare da misalin karfe 3 a ranar Laraba

Kafin mutuwar sa marigayin ya kasance jamiin walwala na kungiyar ta NBA reshen Gusau.

Abubakar ya ce yan bindigar sun lakadawa matar marigayin duka a kokarin a tilasata mata ta nuna inda yake hakan yasa marigayin ya fito daga inda ya buya.

Bayan da yaji ihun matar ne ya sa ya bayyana kansa inda suka ja shi waje suka sassare shi da hakan kuma ya yi sanadiyar mutuwarsa.

More from this stream

Recomended