Yan bindiga sun kashe wani jigon jam’iyar PDP a jihar Osun

Yan bindiga sun kashe, Richard Idowu wani jigo a jam’iyar PDP ta jihar Osun kuma mai neman tsayawa takarar kujerar ɗan majalisar tarayya a karkashin jam’iyar.

Richard wanda aka fi sani da Ade Ori Okin an harbe shi har lahira a cikin wani gini da ba a kammala ba dake wajen garin Ejigbo inda marigayin ya gudanar da wani taron siyasa da yan siyasa da kuma mutanen Ejigbo da yammacin ranar Asabar.

Har ila yau an harbe wani mutum na daban a wani daji dake kusa da gidan da aka harbe ɗan sisayar.

Gwamnan jihar, Ademola Adeleke ya umarci kwamishinan yan sandan jihar da gudanar da bincike domin zaƙulo waɗanda suke da hannu kan faruwar lamarin.

Kwamishinan ƴada labarai na jihar, Oluomo Kolapo Alimi ya roƙi mazauna jihar da su kwantar da hankali inda ya tabbatar musu cewa za a binciki lamarin tare da hukunta wanda suka aikata laifin.

Kawo yanzu dai an kama mutum guda wanda ake zargin yana da hannu a kisan kan.

More from this stream

Recomended