
Yan bindiga sun kashe, Jacob Wodi Hulobu Faston cocin Living Faith dake Aloko-Oganenigu dake ƙaramar hukumar Dekija a jihar Kogi.
Wasu yan bindiga ne da ba a san ko su waye ba suka kai hari kan farmaki kan kauyen a ranar Lahad.
Rahotanni sun nuna cewa faston ya samu nasarar tserewa tare da mabiyansa a yayin harin yan bindigar dai-dai lokacin da suke da tsaka da taron addu’a da asubahi.
A cewar wani mambam cocin mai suna Samuel faston ya koma ne yaga halin da cocin take ciki bayan da kura ta lafa inda anan yan bindigar suka kashe shi.