Yan bindiga sun kashe mutane 7 a cikin masallaci a Kaduna

Akalla mutane 7 aka kashe a ranar Juma’a lokacin da wasu yan bindiga suka kai hari kan wasu masallata a kauyen Saya-Saya dake karamar hukumar Ikara ta jihar Kaduna.

Mansir Hassan mataimakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya ce an kai harin ne da misalin karfe 08:00 na dare lokacin da mutanen suke sallar isha’i.

Hassan ya ce yan bindigar sun harbe mutane 6 a kauyen Saya-Saya inda suka karasa kauyen Tashar Dauda suka kashe karin wani mutum guda a masallaci.

Ya ce mutane uku sun samu rauni a lokacin farmaki kuma yan bindigar sun yi awon gaba da babura huÉ—u.

Mataimakin mai magana da yawun rundunar yan sandan ya ce maharan sun samu nasarar tserewa kafin jami’an tsaro su karasa wurin da lamarin ya faru.

More News

Gwamnatin Abia za ta fara biyan albashi mafi maranci na naira 70,000 a watan Oktoba

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon albashi mafi karanci na naira 70,000 ga ma’aikatanta daga watan Oktoba 2024.Kwamishinan...

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...

Faruk Lawan ya kammala zaman gidan yarin Kuje

An sako tsohon É—an majalisar wakilai ta tarayya, Hon Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje bayan da ya kammala zaman gidan yarin na shekaru...