Yan bindiga sun kashe mutane 4 tare da yin garkuwa da wasu 39 a Abuja da Niger

Mutane hudu aka kashe a yayin da aka yi garkuwa da wasu 39 lokacin da ƴan bindiga suka kai farmaki kauyen Kuduru dake karamar hukumar Bwari a birnin tarayya Abuja da kuma kauyukan Garam da Azu dake jihar Niger mai makotaka da birnin.

A ranar 23 ga watan Disamba ne yan bindigar suka farma Garam dake da tazarar kilomita 5 daga garin Bwari inda suka kashe wani fasto na cocin RCCG tare da yin garkuwa da wasu mutane 13.

Har ila yau a ranar 28 ga watan Disamba yan bindigar suka farma Kuduru wanda yayi iyaka da Garam inda suka yi garkuwa da mutane 18.

Haka kuma a ranar 29 ga watan Disamba yan bindigar suka farma Azu inda suka kashe mutane uku suka kuma yi garkuwa da wasu mutum 8.

Kawo yanzu dai rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja bata fitar da wata sanarwa ba kam faruwar lamarin.

More from this stream

Recomended