Yan bindiga sun kashe mutane 13 tare da sace wasu 73 a Sokoto

Yan bindiga sun kashe mutane 13 tare da sace wasu 73 da suka hada da mata da kananan yara a gabashin jihar Sokoto.

Harin ya faru a kauyuka da dama a kananan hukumomi uku na jihar.

Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Sabon Birni, Goronyo da kuma Gada.

Wakilin jaridar Daily Trust ya rawaito cewa an kai harin ne kusan lokaci daya a kananan hukumomin a ranar Litinin.

Da yake magana da jaridar Daily Trust wani mai rike da sarautar gargajiya a Sabon Birni wanda ya nemi a boye sunansa ya ce kauyuka uku aka kai wa hari a karamar hukumarsa inda aka kashe mutane 11.

Kauyukan sun hada da Gatawa da Dangari inda aka kashe mutane 6, mutum biyu a Gatawa da Kurawa.

More from this stream

Recomended